Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Antediluvians: Occupations of

5 ayoyi · 7 fannoni

Ayoyi game da Occupations of

  1. Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.

  2. Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji.

  3. Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi.

  4. Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa.

  5. Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.