Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adjudication at Law

6 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.

  2. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

  3. kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?

  4. In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani,

  5. in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.

  6. “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.