Nimrod
Ayoyin da suka ambaci Nimrod
Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.
Za su yi mulkin ƙasar Assuriya da takobi, ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi. Zai cece mu daga hannun Assuriyawa sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.