- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Zabura88
Listen to this chapter
0:00
0:00
Rubutun gabatarwa da kiran Allah
1
Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannotmaskil na Heman dangin Ezra. Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.
2
Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.
Kusa da mutuwa da kaɗaici ƙwarai
3
Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari.
4
An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
5
An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka.
6
Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.
7
Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela
8
Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
9
idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.
Maganar kabari
10
Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela
11
Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
12
An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?
13
Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.
Allah da mutum sun yashe ni
14
Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
15
Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
16
Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.
17
Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.
18
Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Options
Study Note