Zabura60
Listen to this chapter
0:00
0:00
Makoki da roƙon sabuntawa
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!
2
Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.
3
Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.
4
Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela
5
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
Maganar sarautar Allah
6
Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.
7
Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina.
8
Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”
Sabon roƙon nasara
9
Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?
10
Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
11
Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.
12
Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Reading Width chars
Options
Study Note