- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ishaya62
Listen to this chapter
0:00
0:00
Adalcin Sihiyona da sabon suna
1
Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
2
Al’ummai za su ga adalcinki, sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki; za a kira ki da sabon suna sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
3
Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji, rawanin sarauta a hannun Allahnki.
4
Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba, ko a kira ƙasarki Kango. Amma za a ce da ke Hefziba ƙasarki kuma Bewula; gama Ubangiji zai ji daɗinki, ƙasarki kuma za tă yi aure.
5
Kamar yadda saurayi kan auri yarinya, haka ’ya’yanki maza za su aure ki; kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa, haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
An naɗa masu tsaro a kan ganuwar
6
Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,
7
kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.
8
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba;
9
amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi su kuma yabi Ubangiji, waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi a filayen wurina mai tsarki.”
An sanar da dawowar mai nasara
10
Ku wuce, ku wuce ƙofofi! Ku shirya hanya saboda mutane. Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku kawar da duwatsu. Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
11
Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’ ”
12
Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Reading Width chars
Options
Study Note