Skip to content

Ezekiyel2

1
Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.”
2
Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana.
3
Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar ’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau.
4
Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’
5
Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu.
6
Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye.
7
Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne.
8
Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”
9
Sai na duba, na kuma ga hannu ya miƙe zuwa wurina. A cikinsa akwai littafi,
10
wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options