Zakariya 8:1-12
1
Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa gare ni.
2
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.”
3
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.”
4
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa.
5
Titunan birnin za su cika da samari da ’yan mata suna wasa.”
6
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.
7
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Zan ceci mutanena daga ƙasashen gabas da yamma.
8
Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.”
9
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku da yanzu kuke jin maganan nan da annabawa suka faɗi, waɗanda suke a nan lokacin da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji Maɗaukaki, bari hannuwanku su zama da ƙarfi don a gama gina haikalin.
10
Kafin wannan lokaci babu albashi domin mutum ko dabba. Ba wanda yake iya sakewa yă yi hidimominsa saboda maƙiya, domin na sa kowa yă zama maƙiyi maƙwabcinsa.
11
Amma yanzu ba zan yi da waɗanda raguwar mutane yadda na yi da na dā ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
12
“Iri zai yi girma da kyau, kuringa za tă ba da ’ya’yanta, ƙasa za tă ba da hatsi, sama kuma za tă ba da raɓa. Zan ba da duk waɗannan abubuwa su zama gādo ga raguwar mutanen nan.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings