Skip to content
Romawa 16:1-5

Romawa 16:1-5

1
Ina gabatar muku da ’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya.
2
Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.
3
Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu.
4
Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai.
5
Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options