Romawa 15:22-29
22
Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.
23
Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku,
24
ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci.
25
Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can.
26
Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima.
27
Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya.
28
Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata.
29
Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.
Settings