Ru’uya ta Yohanna 3:8-11
8
Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba.
9
Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka.
10
Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.
11
Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka.
Settings