Tsallake zuwa abun ciki
Ru’uya ta Yohanna 18:1-3

Mala’ikan Ya Yi Shelar Faɗuwar Babila

Ru’uya ta Yohanna 18:1-3
1
Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa.
2
Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama.
3
Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options