Zabura 78:33-43
33
Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.
34
A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.
35
Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.
36
Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;
37
zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.
38
Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
39
Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.
40
Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji!
41
Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.
42
Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,
43
ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.
Settings