Zabura 73:3-19
3
Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.
4
Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.
5
Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam.
6
Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.
7
Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.
8
Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.
9
Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.
10
Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.
11
Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”
12
Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.
13
Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.
14
Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.
15
Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.
16
Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni
17
sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
18
Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.
19
Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!
Settings