Zabura 73:17-28
17
sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
18
Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.
19
Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!
20
Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.
21
Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,
22
na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.
23
Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana.
24
Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.
25
Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.
26
Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.
27
Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci.
28
Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka.
Settings