Zabura 73:12-22
12
Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.
13
Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.
14
Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.
15
Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.
16
Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni
17
sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
18
Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.
19
Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!
20
Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.
21
Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,
22
na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.
Settings