Skip to content
Zabura 73:1-6

Zabura 73:1-6

1
Zabura ta Asaf. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.
2
Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.
3
Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.
4
Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.
5
Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam.
6
Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.