Skip to content
Zabura 72:6-19

Zabura 72:6-19

6
Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
7
A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
8
Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
9
Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
10
Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.
11
Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
12
Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
13
Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.
14
Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.
15
Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.
16
Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
17
Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.
18
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
19
Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options