Zabura 59:1-7
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
2
Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.
3
Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
4
Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
5
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela
6
Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
7
Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
Settings