Skip to content
Zabura 51:7-12

Zabura 51:7-12

7
Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.
8
Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.
9
Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina.
10
Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
11
Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
12
Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options