Zabura 51:1-6
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.
2
Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina.
3
Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana.
4
Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
5
Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.
6
Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki.
Settings