Zabura 51:13-19
13
Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka.
14
Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka.
15
Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka.
16
Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17
Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
18
Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.
19
Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.
Settings