Zabura 45:12-17
12
Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.
13
Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya.
14
Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.
15
Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki.
16
’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.
17
Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.
Settings