Skip to content
Zabura 44:17-26

Zabura 44:17-26

17
Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.
18
Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.
19
Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.
20
Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,
21
da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?
22
Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.
23
Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.
24
Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?
25
An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa.
26
Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options