Zabura 38:1-11
1
Zabura ta Dawuda. Roƙo ne. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
2
Gama kibiyoyinka sun soke ni, hannunka kuma ya fāɗo a kaina.
3
Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
4
Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.
5
Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi.
6
An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka.
7
Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina.
8
Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata.
9
Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
10
Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna.
11
Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna; maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
Settings