Zabura 35:11-18
11
Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.
12
Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama.
13
Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,
14
nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.
15
Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.
16
Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya.
17
Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki.
18
Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.
Settings