Zabura 119:153-160
153
Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba.
154
Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta!
155
Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka.
156
Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka.
157
Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba.
158
Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka.
159
Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka.
160
Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne.
Settings