Zabura 119:145-152
145
Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.
146
Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka.
147
Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka.
148
Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.
149
Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.
150
Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka.
151
Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne.
152
Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada.
Settings