Zabura 108:1-5
1
Waƙa ce. Zabura ta Dawuda. Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
2
Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.
3
Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.
4
Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari.
5
A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.
Settings