Tsallake zuwa abun ciki
Karin Magana 30:15-17

Karin magana na ƙidaya: Abubuwan da ba sa ƙoshi

Karin Magana 30:15-17
15
“Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’
16
Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’
17
“Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options