Karin Magana 26:1-12
1
Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.
2
Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
3
Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!
4
Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.
5
Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.
6
Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.
7
Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa.
8
Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa.
9
Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa.
10
Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.
11
Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa.
12
Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
Settings