Karin Magana 10:8-14
8
Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci.
9
Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
10
Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci.
11
Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
12
Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
13
Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne.
14
Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.
Settings