Karin Magana 10:1-7
1
Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
2
Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
3
Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.
4
Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
5
Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
6
Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu.
7
Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe.
Settings