Filibbiyawa 2:19-30
19
Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku.
20
Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku.
21
Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.
22
Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.
23
Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan.
24
Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.
25
Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.
26
Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya.
27
Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.
28
Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa.
29
Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa,
30
domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.
Settings