Skip to content
Filemon 1:18-25

Filemon 1:18-25

18
In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina.
19
Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.
20
Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi.
21
Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.
22
Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.
23
Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.
24
Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.
25
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options