Tsallake zuwa abun ciki
Ƙidaya 29:13-38

Ƙidaya 29:13-38

13
A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
14
Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
15
tare kuma da kowane ’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.
16
A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.
17
“ ‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
18
Tare da bijiman, ragunan da ’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
19
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.
20
“ ‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
21
Tare da bijiman, ragunan da ’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
22
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
23
“ ‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
24
Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
25
A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
26
“ ‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
27
Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
28
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
29
“ ‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
30
Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade.
31
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.
32
“ ‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
33
Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade.
34
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
35
“ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba.
36
A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
37
Tare da bijimin, ragon da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
38
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options