Skip to content
Ƙidaya 29:12-16

Hadayu don Idin Bukkoki: rana ta fari

Ƙidaya 29:12-16
12
“ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.
13
A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
14
Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
15
tare kuma da kowane ’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.
16
A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options