Skip to content
Ƙidaya 13:27-33

Ƙidaya 13:27-33

27
Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta.
28
Amma fa mazaunan can ɗin ƙarfafa ne, an kuma kewaye biranen da manya-manyan katanga. Mun kuma ga zuriyar Anak a can.
29
Amalekawa suna zama a Negeb; Hittiyawa, Yebusiyawa da kuma Amoriyawa, suna zama ne a ƙasar tudu. Kan’aniyawa kuma suna zama kusa da teku da kuma a bakin Urdun.”
30
Sai Kaleb ya sa mutane suka yi shiru a gaban Musa, sai ya ce, “Ya kamata mu tafi mu mallaki ƙasar, gama lalle za mu iya cinta.”
31
Amma sauran mutanen da suka je tare da shi, suka ce, “Ba za mu iya kara da mutanen nan ba; sun fi mu ƙarfi.”
32
Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne.
33
Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options