Tsallake zuwa abun ciki
Mika 5:10-15

Ubangiji Ya Tsarkake Isra’ila Ya Hukunta Al’ummai

Mika 5:10-15
10
“A wannan rana,” in ji Ubangiji “Zan hallaka dawakanku daga cikinku, in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.
11
Zan hallaka biranen ƙasarku in yi rugu-rugu da dukan katangunku.
12
Zan kawar da maitarku, ba za a ƙara yin sihiri ba.
13
Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku, nan gaba ba za ku ƙara rusuna wa aikin hannuwanku ba.
14
Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku in kuma rurrushe biranenku.
15
Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options