- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Mattiyu 24:4-11
Alamun farkon wahaloli
4
Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.
5
Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
6
Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.
7
Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.
8
Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.
9
“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.
10
A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,
11
annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.
A cikin nassin nan
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Duba kuma
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
Yohanna 16:2
Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.daga aya ta 9Yohanna 15:19
Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.daga aya ta 9Yohanna 15:20
Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.daga aya ta 9Markus 13:7
Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.daga aya ta 6Markus 13:8
Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.daga aya ta 6Luka 21:16
Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.daga aya ta 9Luka 21:17
Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.daga aya ta 9Ru’uya ta Yohanna 2:10
Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.daga aya ta 9Luka 21:11
Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.daga aya ta 7Luka 21:9
Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”daga aya ta 6Mattiyu 24:11
annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.daga aya ta 5Mattiyu 24:24
Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.daga aya ta 5
Inda wannan ya faru



Bayanin Nazari
Settings