Ba wanda ya san rana ko sa’a
36
“Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
37
Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.
38
Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;
39
ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.
40
Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
41
Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
42
“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.
43
Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.
44
Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.
Settings