Mattiyu 24:1-5
1
Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali.
2
Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”
3
Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”
4
Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.
5
Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
Settings