Mattiyu 21:9-12
9
Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”
10
Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”
11
Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”
12
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.
Settings