Skip to content
Mattiyu 21:12-17

Mattiyu 21:12-17

12
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.
13
Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”
14
Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su.
15
Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.
16
Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”
17
Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options