Mattiyu 21:1-7
1
Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,
2
yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini.
3
In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”
4
Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,
5
“Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”
6
Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.
7
Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu.
Settings