Tsallake zuwa abun ciki
Mattiyu 12:38-45

Mattiyu 12:38-45

38
Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”
39
Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.
40
Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.
41
Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.
42
Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.
43
“Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.
44
Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.
45
Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options