Skip to content
Mattiyu 11:1-10

Mattiyu 11:1-10

1
Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili.
2
Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa
3
su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”
4
Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani.
5
Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.
6
Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”
7
Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?
8
In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke.
9
To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi.
10
Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options