Skip to content
Markus 5:30-41

Markus 5:30-41

30
Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”
31
Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”
32
Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi.
33
Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru.
34
Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”
35
Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”
36
Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”
37
Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub.
38
Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa.
39
Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.”
40
Sai suka yi masa dariya. Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take.
41
Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”).
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options