Markus 15:6-15
6
Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
7
Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.
8
Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.
9
Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10
Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
11
Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
12
Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
13
Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
14
Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
15
Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
Settings