Markus 10:2-9
2
Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”
3
Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”
4
Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”
5
Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.
6
Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’
7
‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,
8
su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.
9
Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”
Settings